
COVID-19: An samu mutum na farko mai dauke da corona a Sokoto
Gwamnatin jihar Sakkwato ta tabbatar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar corona a cikin jihar.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Shine ya bada tabbaci a wata sanarwa da aka watsa a jihar a ranar Litinin.
Rahotanni sun nuna cewa an kwantar da mara lafiyan a asbitin Usman danfodiyo wanda a yanzu haka ke karbar kulawa daga jami'an lafiya.