
Yan Bindiga Sun Sace Mutane 19 a Kauyen Jihar Neja
Rahotanni sun ce an yi garkuwa da mutane 19 daga Kauyen Kutunku da ke cikin Karamar Hukumar Wushishi da ke Jihar Neja.
An ce 'yan bindigar sun isa garin ne da safiyar Litinin, suna harbe-harbe don tsoratar da mutanen kauyen.
Wata majiya a yankin ta shaida wa Aminiya a kiran waya cewa ’yan bindigar sun lakada wa mazauna yankin duka yayin aikin.
Majiyar ta kara da cewa jimillar maza 11 da mata takwas na daga cikin wadanda ‘yan bindigan suka sace.
Ya kara da cewa za a aurar da biyu daga cikin matan da aka sace a karshen makon nan.
Ya kara da cewa 'yan bindigar ba su tuntubi dangin wadanda aka sacen ba.
Jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda, Wasiu Abiodun bai samu damar yin bayani ba har zuwa lokacin wannan rahoton.