
An dage zama tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya sai abinda hali yayi
Zaman da aka shirya yi tsakanin kungiyar Malaman jami'a ta ASUU da gwamnatin tarayya bai yiyu ba a yau.
ASUU tace ba zata samu damar halartar zaman ba saboda ba'a bata isashshen lokacin tuntubar membobinta ba.
Sanarwar hakan ta fitone daga bakin shugaban ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, kamar yanda TheNation ta bayyana.