fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Gwamnonin Arewa

Gwamnoni za su gana da Buhari don magance matsalolin tsaro

Gwamnoni za su gana da Buhari don magance matsalolin tsaro

Siyasa
GWAMNONI na jihohi talatin a karkashin inuwar kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF sun yanke shawarar ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari don magance matsalolin tsaro tare da ci gaba da shari'ar 'yan bindiga, ta'addanci da satar mutane a duk fadin kasar. Gwamnonin na son ganawa da Shugaba Buhari musamman don tattaunawa a makon da ya gabata game da mummunan kisan kiyashin da akayi wa Manoma 43 a kusa da Zarbamari kusa da Maiduguri, Jihar Borno da ’Yan Boko Haram masu tayar da kayar baya yayin da suke aiki a gonakinsu ba tare da wani nau'i na turjiya ba.   Shawarwarin na daga cikin kudurorin da aka cimma a karshen taron tattaunawa na NGF karo na 22
Kungiyar Gwamnonin Arewa sun yi Allah wadai da kisan manoma da Boko Haram ta yi

Kungiyar Gwamnonin Arewa sun yi Allah wadai da kisan manoma da Boko Haram ta yi

Tsaro
Kungiyar gwamnonin Arewa sun bayyana Allah wadai da kisan da Boko Haram tawa Manoma 43.   A sanarwar da shugaban kungiyar Gwamnonin, Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya fitar, yace suna Allah wadai da harin.   Yace harin ba karamar koma baya bane wajan kokarin gwamnati na samar da abinci inda aka kashe manoman ba tare da sun aikata wani laifi ba. Ya bayyana cewa kungiyar tasu zata ci gaba da baiwa jami'an tsaro dukkan goyon bayan da ya kamata dan kawo karshen Lamarin tsaro.