fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: GWAMNONIN NAJERIYA

Kungiyar Kwadago ta Nageriya, ta gargadi gwamnoni su nisanci aro kudi N17trn daga asusun fansho

Kungiyar Kwadago ta Nageriya, ta gargadi gwamnoni su nisanci aro kudi N17trn daga asusun fansho

Siyasa
Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta gargadi gwamnonin jihohi da su guji fitintinar aro daga asusun fansho na Naira tiriliyan 17 don samar da kayayyakin more rayuwa. Kungiyar kwadago ta NLC ta sha alwashin tattara ma’aikatan Najeriya a duk fadin kasar don nuna rashin amincewarsu da duk wani yunkuri da gwamnoni ke yi na karbo bashin daga kudin, inda suka ce amfanin fansho ne na ma’aikata.   Shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Ayuba Wabba ya fadi haka ne a taron Majalisar Zartarwa ta Kasa (NEC) karo na 47 na kungiyar Likitocin da Ma’aikatan Lafiya na Nijeriya (MHWUN) a ranar Alhamis a Abuja.