fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Tag: Gwannan Kano

Gwamnatin jihar Kano ta tallafawa masu fama da cuta mai karya garkuwar jiki Da horon sana’o’i

Gwamnatin jihar Kano ta tallafawa masu fama da cuta mai karya garkuwar jiki Da horon sana’o’i

Uncategorized
Gwamnatin jihar Kano ta horar tare da baiwa mutane 250 masu dauke da cutar kanjamau da sauran wasu kungiyoyi horo kan dabarun koyon sana'oi daban-daban. Darakta Janar na Hukumar Kula da masu cuta mai karya garkuwar jiki na jihar kano Sabitu Shu'aibu Shanono ya ce bayar da tallafin zai magance tsananin talauci da rashin aikin yi tsakanin wadanda ke fama da cuta mai karya garkuwar jiki a jihar. Mista Shanono ya bayyana cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje shine ya kaddamar da shirin a ranar 1 ga Disamba, a dakin taro na Coronation, dake gidan Gwamnatin jihar A wani bangare na bikin ranar yaki da cutar kanjamau ta duniya da aka gudanar. Mista Shanono ya bayyana cewa mahalarta taron an horar da su sana'o'i daban-daban da suka hada da Dinki kwalliya da sauransu. A nasa jawabin, Shugab...
Gwamna Abudullahi Umar ganduje ya gana da shugabannin kiristoci dake jihar kano CAN

Gwamna Abudullahi Umar ganduje ya gana da shugabannin kiristoci dake jihar kano CAN

Kiwon Lafiya
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya nemi goyon bayan shugabanin kungiyar Christain Association of Nigeria (CAN) a cikin jihar domin shawo kan yaduwar cutar COVID-19. Ganduje, wanda ya gana da shugabannin kungiyar a Gidan Gwamnati, Kano, ranar Talata, ya ce hadin gwiwar masu ruwa da tsaki ya zama dole domin dakile yaduwar cutar. Gwamnan ya yi kira ga shugabanni da sauran mazauna yankin da su yi taka-tsan-tsan ga matakan kula da lafiya. Gwamnan ya yabawa shugabancin kungiyar CAN sabuda rashin nuna banbanci a zamantakewa. Shugaban CAN na jihar, Rev. Samuel Adeyemo, ya godewa gwamnan tare da yaba masa kan kokarin da yake wajan dakile yaduwar cutar a jihar Kano. A karshe gwamanan kano yayi al'kawarin Samar da cibiyar gwaje-gwaje a yankin sabon gari dake jihar Kano
Shehu Sani ya roki Gwamna Ganduje ya yafewa Sarki Sanusi

Shehu Sani ya roki Gwamna Ganduje ya yafewa Sarki Sanusi

Siyasa
Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, a ranar Juma’a ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje da ya gafarta wa Mai Martaba Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sanusi ll.   Shehu ya bukaci Ganduje da ya gafarta ma Mai Martaba Sarki saboda Ikon gwamna na dan lokaci ne. A cikin wani sakon Twitter, tsohon dan majalisar ya nuna cewa Ganduje na iya neman taimakon Sanusi idan ya sauka daga mukamin nasa, don haka ya kamata a yafe mashi. Jiya ne dai  Hukumar Kula da korafe Korafan Jama'a da Laifin Cin Hanci da Rashawa ta Kano, ta dage kan lallai sai Sanusi ya bayyana a gabanta bisa zargin karkatar da makudan kudade