fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Hadarin Jirgi

Shugaba Buhari ya mika sakon jaje ga iyalan da Jirgi me saukar Angulu ya fadawa a Legas

Shugaba Buhari ya mika sakon jaje ga iyalan da Jirgi me saukar Angulu ya fadawa a Legas

Siyasa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya miƙa saƙon ta'aziyarsa ga iyakan waɗanda suka mutu a hatsarin helikwafta da ya faru yau a Legas. A wata sanarwa da Femi Adesina mai bai wa Buhari shawara kan harkar yaɗa labarai ya fitar ya ce shugaban ya kuma ce a yayin da ake jiran sakamakon binciken abin da ya jawo hatsarin, shugaban na addu'ar Allah Ya bai wa iyalan mamatan haƙurin rashinsu, tare da bai wa marasa lafiya sauƙi. A yau Juma'a ne helikwaftan ya yi hatsari a garin Legas da ke kudancin Najeriya. Rahotanni sun ce aƙalla mutum biyu suka mutu a hatsarin inda jirgin ya faɗi a ginin wata coci ta sojoji a unguwar Opebi cikin Ikeja.