
Hadarin mota a Kano ya yi sanadiyyar mutum biyu, yayin da mutane biyar suka jikkata
An tabbatar da mutuwar mutum biyu yayin da wasu biyar suka jikkata a wani hatsarin mota a kan hanyar Kano zuwa Zariya da ke kauyen Dakatsalle.
Kwamandan sashin na FRSC a jihar Kano, Mista Zubairu Mato, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, NAN ta ruwaito.
Mato ya ce hatsarin ya rutsa da motar kirar Peugeot 306 mai lamba TFA 429 TJ da tirela mai lamba KTJ 574 XA.
A baya dai, hutudole.com ya kawo muku yanda hadarin mota ya ci rayuka da yawa a Bauchi.
“Mun samu kiran waya da misalin karfe 3:15 na safiyar ranar 29 ga Maris, 2021.
"Da samun wannan bayanin, muka hanzarta tura jami'ai da motocinmu zuwa wurin da abin ya faru domin ceton wadanda abin ya shafa da karfe 3:40 na safe."
Kwamandan sashen ya kara da cewa hatsarin ya afku ne sakamakon saurin ...