
Hadarin Mota Yayi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 2 A Jihar Kano
Kusan kwana uku bayan da mutane hudu suka rasa rayukansu a cikin Kano, wasu mutane biyu sun mutu a ranar Laraba lokacin da motoci uku sukayi taho mugama a Titin Panshekara a cikin birnin.
A cewar kakakin Hukumar Kula da Haddura ta Tarayya a jihar, Kabir Daura, hadarin ya faru ne a kan layin Panshekara na babbar hanyar mota.
A cewarsa, hadarin ya shafi wata motar dauke da dabbobi, Toyota Space Wagon da babur mai kafa uku, wanda aka ce matukin ta yana tukin gan ganci a gaban motar.
Daura ya ce, "A kokarin kaucewa wannan babur din, direban motar ya kutsa cikin wata mota da babur din, ya ja su zuwa shagon da ke gefan titin, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu, wani dattijo da kuma wata yarinya mace."
Jim kadan bayan hadarin, ya ce jami'an hukumar FRSC sun kwas...