
An zargi Dangote da aikawa Hadiza Bala Usman Miliyan 200 a lokacin zaben 2015
Wasu Rahotannin sirri sun bayyana cewa a lokacin zaben 2016, attajirin me kudin Africa, Aliko Dangote ya aikewa da Hadiza Bala Usman Miliyan 200 cikin Asusun Bankinta.
Rahoton wanda Peoplesgazette ta ruwaito yace an yi amfani da bankin Access wajan aika da kudin inda aka fara aika Miliyan 100 sannan daga baya aka kara aika sauran.
Majiyar tace, Kokarin jin ta bakin Dangote akan lamarun ya ci tura inda kakakinsa, Tony Chiejina bai tabbatar ko karyata lamarin ba.
Saidai a bangaren Hadiza Bala Usman tace bata san da wannan lamari ba na tura kudin. Ana zargin dai Hadiza ta taka Rawar gani sosai wajan yakin neman zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari a shekarar 2015 amma ta bayan fage.