
Coronavirus/COVID-19 Hotuna:Rahama Sadau da Hadiza Gabon sun rabawa Mabukata Abinci
Taurarin fina-finan Hausa,Rahama Sadau da Hadiza Gabon sun rabawa mabukata abinci a jihar Kaduna.
Hadiza Gabon wadda dama ta saba tallafawa mabukata a karkashin Gidauniyarta ta Hadiza Gabon Foundation da abokiyar aikinta, Rahama Sadau sun kai kayan Abinci ga Mabukata a unguwar Rimi dake jihar Kaduna.
https://www.instagram.com/p/B-uHsOeH64Y/?igshid=7x7q397k4til
Shafin gidauniyar Hadiza Gabon dinne ya bayyana haka, kamar yanda za'a iya gani a sama.
Masu hannu da shuni da yawane da kamfanoni da gwamnati a wannan halin da ake ciki na matsin da Cutar Coronavirus/COVID-19 ta saka mutane a ciki ke bayar da tallafi ga mabukata.