
Hukumar Kiyaye Hadura Ta Kasa, FRSC Ta Mayar Da N900,000 Ga Iyalan Wadanda Hadarin Ya Ritsa Da Su A Jihar Nasarawa
Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC), Yankin Nasarawa, ta ce ta mayar da N900,000 ga wadanda hadarin ya rutsa da su a ranar Litinin.
Kwamandan Yankin, Hammed Mohammed, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba, ya ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 4:00 na yamma. a Sabon-Gida kan babban titin Keffi zuwa Garaku, Jihar Nasarawa.
Mista Mohammed ya ce hadarin ya hada motar Volkswagen Sharon da ke dauke da fasinjoji shida a kan hanyarsu daga Jos zuwa Abuja.
A cewarsa, jami’an ceto na hukumar FRSC sun isa wurin da hadarin ya faru cikin mintuna bakwai da samun labarin lamarin.
Mista Mohammed ya ce: “Ana kyautata zaton hadarin ya faru ne sakamakon gudu wanda kuma yayi sanadiyyar mutuwar direban motar, Mista Suleiman da wani saurayi daya.
“Sauran fasinjojin d...