
Yanda Hafsat Idris ta aurar da diyarta ta 3
Tauraruwar finafinan Hausa Hafsat Idris ta aurar da ɗiyar ta ta uku a ƙarshen gagarumin bikin da aka ɗau kwanaki ana yi a birnin Kano.
Hafsat, wadda ake yi wa laƙabi da ‘Ɓarauniya’, ta aurar da Khadija Kabir ne ga wani matashi mai suna Abubakar Ibrahim Muhammad.
An ɗaura auren da misalin ƙarfe 12:00 na rana a unguwar Ɗandago cikin ƙwaryar Kano a kan sadaki N50,000.
Taron ɗaurin auren ya samu halartar ɗimbin ‘yan’uwa da abokan arziki, amma mujallar Fim ba ta ga fuskar abokan sana’ar uwar amarya a wurin ba.
To sai dai sun yi mata kara a sauran shagulgulan da aka gudanar, ciki har da liyafar cin abincin dare da aka yi a shekaranjiya Juma’a, 26 ga Maris, 2021 a wurin taro na Fabs da ke Kano.
Ɗimbin ‘yan’uwa da abokan arziki sun halarci...