fbpx
Sunday, December 4
Shadow

Tag: Hajiya Hadiza isma’il

Mijina Ba ‘Mijin Ta Ce’ Ba Ne>>Uwargidan Gwamna El’rufa’i

Mijina Ba ‘Mijin Ta Ce’ Ba Ne>>Uwargidan Gwamna El’rufa’i

Siyasa
Hajiya Hadiza El'rufa'i ta wallafa wani rubutu Cikin raha da barkwanci a shafinta na Twitter tana Mai cewa baki dayan Kai kawona a Cikin dakin Za OZA, El'rufa'i ya zabi namiji a sarautar Zazzau yanzu duk Duniya kowa Yasan bani da tasiri akan mijina, shi ba mijin Hajiya bane shi ba mijin tace bane. Masu karatu idan baku manta ba uwar Gidan Gwamna dai kwanaki ta nuna ra'ayinta Kan a maye gurbin sabon Sarkin Zazzau da mace..
Uwar gidan gwamnan kaduna ta godewa al’umma bisa addu’ar da su kaiwa mijin ta

Uwar gidan gwamnan kaduna ta godewa al’umma bisa addu’ar da su kaiwa mijin ta

Uncategorized
Matar gwamnan kaduna Hadiza isma'il el'rufai ta bayyana farin cikin ta da samun saukin mijin ta daga cutar Covid-19 inda ta godewa al'umma bisa dumbin addu'ar da su kaiwa mijinta tare da fatan samun sauki ga wadan da basu warke daga cutar ba. https://twitter.com/hadizel/status/1252943612763127808?s=20 Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya murmure daga cutar Covid-19 wadda aka fi sani da coronavirus. Sanarwar hakan ta fito ne ta shafinsa na sada zumunci a ranar Laraba. Inda ya bayyana farin cikin sa bayan ya shafe tsawan ma kwanni biyu a killace, wanda bayan gwajin da a kai masa sakamakon na sa ya bayyana ya warke daga cutar.
Sakamakon gwajin matar Gwamnan kaduna ya fito

Sakamakon gwajin matar Gwamnan kaduna ya fito

Kiwon Lafiya
Uwar gidan gwamnan Kaduna Malam Nasiru El Rufa'i Hajiya Hadiza Isma El-Rufai, biyo bayan gwajin da akai mata a ranar lahadi a yau sakamakon nata ya fito inda sakamakon nata ya nuna cewa bata kamu da cutar Covid-19 ba. Tun bayan sanarwar da mai gidan ta ya bayar cewa ya kamu da cutar Coronaviru a ranar asabar, biyo bayan haka sai Uwar gidan nasa itama aka tabbatar da yi mata gwaji domin duba lafiyarta wanda daga bisani ne rahoto ya bayyana bata dauke da cutar. A ranar litinin ne uwar gidan gwamnan ta bayyana a shafinta na sada zumunci cewa sakamakon gwajin da akai Mata ya nuna bata dauke da cutar. Bayan bayyanar hakan itama cibiyar kula da cututtuka ta kasa ta bayyana Kara samun sabbin wanda suka kamu da cutar har kusan mutum 20 wanad biyu daga cikin su yan jihar kaduna ne.