fbpx
Sunday, May 22
Shadow

Tag: Hajja

Covid-19: Kasar Indonesiya ta dakatar da Mahajjatan kasar  zuwa aikin hajjin bana

Covid-19: Kasar Indonesiya ta dakatar da Mahajjatan kasar zuwa aikin hajjin bana

Kiwon Lafiya
Ministan kula da harkokin addini na kasar Indonesiya Fachrul Razi a ranar Talata ya bayyana soke tafiyar mahajjatan kasar don halartar aikin hajjin bana. Fachrul ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai a Jakarta, inda ya ce gwamnati ta yanke shawarar soke aikin Hajjin wannan shekara ne bisa gazawar hukumomin kasar Saudi wajan bayar da tabbabaci a game da aikin. Ministan ya ce sun yanke wannan shawarar ne tare da yin duba sosai, musamman game da batun kiwon lafiya. Indonesiya tana da yawan mahajjata da aka tantance da suka kai kimanin mutum  221,00 a wannan shekara. Hakanan itama  kasar Singapur ta sanar da dakatar da aikin hajjina bana a watan da ya gabata, inda ta bayyana cewa 'yan kasarta ba za su yi aikin Hajjin bana ba a sakamakon barkewar cutar coronavirus.