
Hukumar Alhazai ta jihar Kwara ta sanar da ranar da za a fara shirye-shiryen aikin Hajji na 2021
Hukumar jindadin al'hazai ta kwara ta ce shirye-shiryan aikin hajji na 2021 ga maniyyatan dake son tafiya aikin hajjin shekara mai zuwa zai fara a ranar 7 ga watan satumba.
Alhaji Mohammed Tunde-Jimoh, Sakataren zartarwa na hukumar, shine ya bayyana hakan a wata hira da yai da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Ilorin ranar Talata.
Tunde-Jimoh ya bayyana cewa, hukumar tayi tsari mai kyau na naganin ba'a samu tsaiko ba ga maniyyatan da ke shirin zuwa aikin hajjin shekarar mai zuwa.
A cewar sa, 100 ne kawai daga cikin 1,800 suka nemi da a mayar musu da kudadan su na hajjin shekarar 2020, dan haka a cewar sa raguwar da suka rage 1,700 da basu karbi kudadan su ba sune hukumar zata fara shigarwa.
Ya kara da cewa, wadanda suka bar kudadan su lalle suny...