fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Hajjin Bana

Yanda ake gudanar da aikin Hajjin Bana

Yanda ake gudanar da aikin Hajjin Bana

Uncategorized
Tuni aka fara gudanar da aikin Hajjin bana wanda mahajjata dubu 10 suke gudanarwa.   Shafin Haramain ya bayyana cewa an kammala Dawafil Qudum wanda ake yi bayan Isa Makkah.   Saboda cutar Coronavirus data bulla a Duniya mahajjatan sun yi Nesa-nesa da Juna yayin da suke gabatar da aikin Ibadar. https://twitter.com/HaramainInfo/status/1288397558667030528?s=19
Sarkin Musulmi yayi kira ga wanda suka yi niyyar zuwa hajjin bana su taimakawa talakawa da kudin hajjin

Sarkin Musulmi yayi kira ga wanda suka yi niyyar zuwa hajjin bana su taimakawa talakawa da kudin hajjin

Siyasa
Me alfarma Sarkin Musulmi,  Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bayyana taya Musulmai Murnar Babbar sallah inda yayi kira ga mutane cewa a bi dokokin hana yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.   A sanarwar da majalisar Koli ta addinin Musulunci da Sarkin ke jagoranta ta fitar ta hannun sakatarenta, Farfesa Salihu Shehu, Sarkin Yayi kira ga mutane su bi dokokin garuruwan da suke a lokacin Sallar Idi. Yace kada mutane su tada hankalinsu cewa dole sai sun yi sallar Idin saboda ba farilla bace idan hakan zai iya jawo matsala.   Sarkin yayi kira ga masu halin da suka yi niyyar zuwa hajjin bana amma basu samu wan ba da su bayar da sadakar wadannan kudi ga mabukata san samun lada.   Sarkin ya bayyana cewa, ga wanda ke da niyyar bada sadakar amma bai san inda ya ka...
Mutane Dubu 1 ne kawai za’a bari su yi hajjin Bana>>Saudiyya

Mutane Dubu 1 ne kawai za’a bari su yi hajjin Bana>>Saudiyya

Uncategorized
Kasar Saudiyya ta bayyana cewa mutanen dake kasashen waje ba zasu yi aikin Hajjin Bana ba, 'yan kasarne kawai za'a bari su yi.   Wannan ne karon farko cikin shekaru kusan 90 da aka taba samun hakan a Saudiyya.  Ministan Hajji, Muhammad Benten ya bayyana cewa ba zasu bar mutane da yawa su yi aikin hajjin ba inda yace suna kan tattaunawa. Yace watakila su kai mutum Dubu 1 wata kila ba zasu kai ba ko kuma su fi haka.   Yace kamin su shiga aikin Hajjin sai an killace su sannan bayan sun gama ma sai an kullacesu. Sannan yace ba za'a bar wanda suka kai shekaru 65 shiga aikin Hajjin ba
Hajjin Bana: Har mun karɓi kuɗaɗen maniyyata aikin bana>>Najeriya

Hajjin Bana: Har mun karɓi kuɗaɗen maniyyata aikin bana>>Najeriya

Uncategorized
Hukumar aikin hajji ta Najeriya ta ce za ta yi wani taro a ranar Talata, don sanin mataki na gaba da za ta ɗauka, bayan Masarautar Saudiyya ta sanar da jingine aikin hajjin bana ga maniyyatan ƙetare.   Ta ce duk da shawarwarin hukumomin Saudiyya a watan Maris, na a dakatar da shirye-shiryen aikin hajjin bana, a Najeriya, an ci gaba da wasu shirye-shiryen ibadar ta shekara-shekara.   "Tun watan uku da muka ga haka, mu ba mu so a ce mu daina (shirye-shirye) kwata-kwata ba. Saboda kada a zo daga baya a ce za a yi wannan aikin hajji, kuma a yi mana ba-zata," in ji hukumar.   Kwamishinan ayyuka a hukumar, Alhaji Abdullahi Magaji Harɗawa ya ce matakin na ƙasar Saudiyya bai zo musu da mamaki ba, duk da yake sun shafe tsawon watanni a cikin zulumi.   Ya ce...