
Abokiyata ce kawai, ba aurenta zan yi ba>>Tsohon Minista, FFK yayi karin haske kan labarin aurensa da tauraruwar fina-finan Hausa,Halima
A baya mun samu labari daga Kemi Olunloyo cewa Tsohon Ministan Sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode zai auri tauraruwar fina-finan Hausa, Halima Yusuf.
Kemi tace Femi da Halima sun shafe kusan shekara daya tare kuma a yanzu yana shirin aurenta a matsayin matarsa ta 5.
Saidai a martaninsa, Femi Fani Kayode ya karyata wannan ikirari inda yace shi da Halima abokaine kawai, babu maganar aure a tsakaninsu.
Yace ita da sauran wasu abokansa suna matukar kwantar masa da hankali inda yace shiyasa yake ganin kimarta. Ya kara da cewa masu maganar cewa zai aureta su daina, ba gaskiya bane.