Sunday, March 29
Shadow

Tag: Hamisu Breaker

Ban Sa A Kama Hamisu Breaker Ba>>Adam Fasaha

Ban Sa A Kama Hamisu Breaker Ba>>Adam Fasaha

Wasanni
Fitaccen mawakin nan, Adam Fasaha ya musanta jita-jitar da ake ta yadawa cewa ya kama abokin sana'arsa mawaki Hamisu Breaker bisa zargin sa sa yaudaro tsohuwar matarsa, Momi Gombe zuwa cikin masana'antar fim.     Idan ba a manta ba, tun bayan da Adam Fasaha ya zargi Hamisu Breaker din ne aka soma yada wasu hotuna da aka nuna jami'an tsaro sun kama mawaki Breaker, wanda kuma hotunan an yi su ne da sunan wasa a yayin wani wasa da Breaker ya gudanar a cibiyar wasanni ta Abacha Youth Center dake Kano a shekarun baya.     A yayin da yake jawabi ta bakin Adam Fasaha, mawaki Aliliyo Mai Waka ya bayyana cewa wasu daga cikin yaran Hamisu Breaker din ne suke ta yada hotunan domin su jawowa Adam Fasaha zagi.     "Ni Aliliyo Mai waka ina da tabb...
Kazafin Da Aka Yi Min Na Mu’amàla Da Matar Aure, Na Dauke Shi A Matsayin Jarabta Daga Allah, Cewar Hamisu Breaker

Kazafin Da Aka Yi Min Na Mu’amàla Da Matar Aure, Na Dauke Shi A Matsayin Jarabta Daga Allah, Cewar Hamisu Breaker

Nishaɗi
Shahararren mawakin finafinan Hausa, Hamisu Sa'idu Yusuf wanda aka fi sani da Hamisu Breaker ya bayyana cewa batun da aka danganta shi da shi na cewa ya yaudari wata matar aure zuwa masana'antar finafinan Hausa ya dauki lamarin a matsayin kazafi kuma jarabta daga Allah. Kuma yana fatan Allah ya sa ya ci wannan jarabawar.   Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata wani mawaki mai suna Aliliyo Mai Waka ya zargi Hamisu Breaker da laifin yaudaro wata matar takwaransa mawaki Adam Fasaha zuwa cikin harkar fim.   An yi zargin cewa tun kafin jarumar mai suna Momee Gombe ta fito daga gidan mijinta mawaki Breaker yake hure mata kunne, wanda kuma bayan fitowar ta din ne aka soma ganin yana saka ta a bidiyon wakokinsa, wanda hakan ya sa aka sake tabbatar da zargin da ake yi masa....
An Zargi Mawaki Hamisu Breaker Da Yaudaro Matar Aure Zuwa Cikin Harkar Fim

An Zargi Mawaki Hamisu Breaker Da Yaudaro Matar Aure Zuwa Cikin Harkar Fim

Nishaɗi
Ana zargin shahararren matashin mawakin finafinan Hausa, Hamisu Breaker Dorayi da laifin hurewa wata matar aure kunne har sai da ya yaudaro ta zuwa cikin harkar fim din Hausa. Ba kowa bace ake zargin Breaker ya hurewa kunnen illa yarinyar da ake yawan ganin yana daukar wakokin bidiyon sa da ita, wato Momee Gombe. Rahotanni sun tabbatar da cewa Momee Gombe ta taba auren daya daga cikin mawakan Hausa, wato Adam Fasaha wanda kuma na hannun daman Hamisu Breaker din ne. A yayin jin ta bakin na hannun daman Adam Fasaha, wato Aliliyo Mai Waka, ya bayyana cewa shekaru biyu da suka gabata, Adam Fasaha ya auri Momee Gombe, amma sai Hamisu Breaker ya dinga hure mata kunne ba tare da ya yi laka'ari da cewa tana gidan miji ba, inda har ta kai ga asirin sa ya tonu har ya nemi gafarar abokin nas...