fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Tag: Hanan Buhari

Bidiyon yanda Hamisu Breaker ya cashe a bikin diyar shugaban kasa, Hanan Buhari

Bidiyon yanda Hamisu Breaker ya cashe a bikin diyar shugaban kasa, Hanan Buhari

Uncategorized
Tauraron mawakin Hausa, Hamisu Breaker ne yayi wasa a wajan bikin diyar shugaban kasa, Hanan Buhari da Angonta, Turad Sha'aban inda yayi shahararriyar wakarsa ta Jarumar Mata.   Breaker ya saka kadan daga cikin bidiyon yanda wasan ya kasance a shafinsa na Instagram inda aka ganshi yana wake Ango da Marya. https://www.instagram.com/p/CE2Kh0xJvGk/?igshid=x2yf13amqrvk Ya musu Addu'ar Allah ya sanya Alkhairi Muhammad Turad da Hanan Buhari.
A’isha Buhari ta caccaki Daily Trust kan zanen da ta yi akan bikin diyarta, Hanan

A’isha Buhari ta caccaki Daily Trust kan zanen da ta yi akan bikin diyarta, Hanan

Uncategorized
Uwargidan shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari ta mayar da martani kan zanen barkwancin da jaridar Daily Trust ta yi akan bikin diyarta, Hanan Buhari da Angonta, Turad, Sha'aban.   Dailytrust ta wallafa hoton wanda ya nuna A'isha Buhari tana nunawa 'yan Najeriya hotunan Bikin Diyarta, Hanan Buhari yayin da su kuma aka nunasu cikin wahala. Saidai A'isha Tace hakan da ta yi na saka hotunan bikin auren diyartata ba wai dan isgili bane ga 'yan Najeriya, kawaidai dan tawa wanda suka taya ta hidimar bikin godiya ne.   Me magana da yawun matar shugaban kasar, Aliyu Abdullahi ne ya bayyanawa BBC Pidgin haka a hirar da suka ti dashi.   Saidai A'isha ta bayyana cewa kasancewar shugaba Baya wa mutane abinda suke so bai hana 'ya'yanshi yin aure.
Bidiyon yanda aka yi ruwan kudi a bikin diyar shugaban kasa, Hanan Buhari da Angonta Turad

Bidiyon yanda aka yi ruwan kudi a bikin diyar shugaban kasa, Hanan Buhari da Angonta Turad

Nishaɗi
Wadannan hotunane da Bidiyo da suka bayyana yanda aka yi wasa da Nera a bikin diyar shugaban kasa, Hanan Buhari da Angonta Turad, masu iya magana na cewa, Wani ma yayi rawa ballantana dan makadi.   A ranar Juma'ar data gabata ne dai aka daura auren masoyan a fadar shugaban kasa dake Abuja, irinsa na farko wanda ya samu halartar 'yan uwa da abokan arziki da suka hada da gwamnan Kaduna, Mataimakin Shugaban kasa, dadai sauransu.    
Dan Fulani da yaso auren diyar shugaban kasa, Hanan Buhari da sadakin Shanu 150

Dan Fulani da yaso auren diyar shugaban kasa, Hanan Buhari da sadakin Shanu 150

Uncategorized
Abdullahi Bashir dan kimanin shekaru 22 daga jihar Adamawa, Yola na daga cikin wanda suka so auren diyar shugaban kasa da aka daurawa aure jiya watau Hanan Buhari.   Ya bayyana cewa a hoto ya fara ganinta a lokacin da ta je jihar Bauchi wajan bikin daukar hoton da ta yi na kammala karatunta. Yace ta matukar birgeshi musannan yanda ya ga a matsayinta na diyar shugaban kasa ta dauki sana'ar daukar hoto wanda ko a kasashen turawa da suka waye ba'a cika samun haka ba.   Ya bayyanawa Daily Trust a hirar da suka yi dashi cewa da farko be san diyar shugaban kasa bace amma daga baya da yaji cewa diyar shugaba Buhari ce duk da haka gwiwarsa ba ta yi sanyi ba. Ya kudurce a ransa cewa sai ya cimma burinsa na gaya mata irin son da yake mata koda kuwa ba zata amince ba ku...
Hotuna da Bidiyon yanda aka daura auren diyar shugaban kasa, Hanan Buhari da Angonta, Turad, El-Rufai, Ahmad Lawal, Femi Gbajabiamila sun halarta

Hotuna da Bidiyon yanda aka daura auren diyar shugaban kasa, Hanan Buhari da Angonta, Turad, El-Rufai, Ahmad Lawal, Femi Gbajabiamila sun halarta

Nishaɗi
A jiya, Juma'a ne aka daura auren diyar shugaban kasa, Hanan Buhari da Angonta, Muhammad Turad a fadar shugaban kasar, dake Abuja.   Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammad Sanusi ne waliyyin Amarya inda wakilin sarkin Zazzau ya zama wakilin Ango.   Taron daurin auren wanda bai tara jama'a da yawa ba ya samu halartar manyan mutane irinsu, Mataimakin shugaban kasa,  Farfesa Yemi Osinbajo,  kakakin majalisar wakilai,  Femi Gbajabiamila,  dana majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawal da gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai dadai sauransu.
Matashin da yayi barazanar kashe kansa idan Diyar shugaban kasa, Hanan Buhari bata aureshi ba ya fasa bayan da ‘yansanda suka bashi hakuri

Matashin da yayi barazanar kashe kansa idan Diyar shugaban kasa, Hanan Buhari bata aureshi ba ya fasa bayan da ‘yansanda suka bashi hakuri

Nishaɗi
Matashi Abba Ahmad dake ajon karshe na jami'ar Yusuf Maitama Suke dake Kano wanda a baya yayi barazanar kashe kansa muddin bai samu auren diyar shugaban kasa, Hanan Buhari ba a yanzu bayan an daura mata aure ya hakura.   Matashin ya hakura ne bayan da 'yansanda suka gayyaceshi tare da kuma bashi baki. Kakakin 'yansandan jihar Kano, Abdullahi Haruna ya tabbatar da faruwar Lamarin inda yace matashin dan shekaru 22 ya kuma yi magana da kakakin 'yansanda na kasa, Frank Mba. Yace sun shafe sama da mintuna 6 suna magana ta waya da kakakin 'yansandan na kasa inda ya gayawa Abba cewa kada ya kashe kansa kumama Addininsa ya hana mutum ya kashe kansa idan bai samu auren Hanan Buhari ba.   Matashin ya amince da wannan shawara har ma ya nuna sha'awarsa da shiga aikin dansa...