
Kungiyar Masu kula da gidaje zasu kai Gwamnati kotu kan sakawa Masu zaman gidajen haya Haraji
Kungiyar masu kula da gidaje ta NIESV ta bayyana cewa idan bata samu cikakken bayani kan sabon harajin da masu zaman gidajen haya zasu rika buya ba, zata garzaya kotu.
Shugaban kungiyar, Emma Wike ne ya bayyana haka inda yace sun yadda da gwamnati ta samar da hanyoyin samun kudin shiga amma maganar gaskiya kudin harajin da ake shirin sakawa masu gidajen hayar yayi yawa.
Yace zasu je kotu su nemi a musu bayani kan sabon harajin sannan kuma a mayar dashi Dubu 1 kawai ga kowane me biyan haya.
Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kula da karbar haraji ta FIRS ta saka kaso 6 cikin 100 kan masu zaman gidajen haka da suka kai shekaru 7 zuwa 20 da kuma kan C od O.
Saidai Wike yace wannan tsari musamman a yanzu da mutane ke jin jiki bai yi ba.