
Adadin Mutanen Da Aka Kashe Tsakanin Sokoto, Zamfara Da Katsina A Cikin Makonni Biyu Da Suka Gabata Sun Haura 800>>Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun
Fittacen malamin addinin musulunci dake garin Kaduna mataimakin shugaban Majalisar Malamai na 'kasa na Kungiyar Izalah, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya bayyana takaicinsa kan yadda ake kashe al'umma a jihohin Katsina, Sokoto Zamfara inda yace alissafin da ya yi a kasa da makonni 2 kadai an kashe sama da mutane 850.
Sheikh Rigachikun ya ce baya ganin laifin shugaban kasa a tabarbarewar tsaro a yankin Arewa, ya ce shugaban kasa ya bawa Arewa dukkan wani mukami a bangaren tsaro sune suka ki yin abunda ya dace.
Sheikh Rigachikun ya kara da cewa kisan ran Dan Adam babbban laifi ne a wajen ubangiji. Ya ce ya fi sauki mutum ya rushe dakin ka'aba akan ya kashe ran mumini daya.
Yace Manzon Allah S A W yace "duk wanda ya taimaka aka kas...