
An sace motar Range Rover ta Fam Dubu 100 mallakin Dan kwallon Tottenham, Harry Kane
Wasu barayi sun sace motar tauraron dan kwallon kasar Ingila, Harry Kane. Motar kirar Range Rover ce da kudinta suka kai Fan Dubu 100.
Rahotanni sun bayyana cewa barayin sun yi ta zuwa suna zowa kamin daga baya su sace motar su tsere da ita.
An sace motarne a watan October a ChingFord, Estern London bayan an ga wata mota na zuwa tana wuceta akai-akai.
Majiyar 'yansanda ta gayawa Sun cewa an bayyanawa Harry Kane cewa da wuya a gano motar tasa. Barayin sun yi amfani da wata na'urane wajan bude motar. Kane yace farin cikinsa daya shine ba'a jiwa kowa ciwo ba kuma barayin basu dauki wani abu da ba za'a iya maye gurbinsa ba.
Kane na daukar Albashin Fam Dubu 200 duk Mako.
'The way the robbery played out didn't feel like a coincidence.'
T...