
Ingila ta cire Harry Maguire daga cikin tawagar ta bayan kotu ta yanke mai hukuncin watanni 21 a gidan yari
Ingila ta cire dan wasan baya na kungiyar Manchester Harry Maguire daga cikin tawagar ta da zasu kara da kasar Iceland da Denmark a gasar kofin kasashe, bayan kotu ta kama shi da dukkan laifin da ake tuhumar shi da kamun data yi mai kuma har yayi yunkurin bayar da cin hanci.
Manajan tawagar Ingilan Gareth Southgate ya saka sunan kaftin din Machestan daga farko kuma har yace ya tattauna da Maguire akan wasannin, amma bayan wasu awanni aka gano cewa dan wasan mai shekaru 27 yana da laifi bayan ya bar kasar Greece kuma har aka yanke mai hukuncin watanni 21 da kuma kwanaki 10 a gidan yari, amma an dakatar da wannan hukuncin.
Sakamakon wannan hukuncin yasa Gareth Southgate ya cire sunan dan wasan Manchester United din a cikin tawagar shi har na wasanni biyu da zasu buga a watan satumba.