
Yan Najeriya miliyan 25 za su rika biyan N4,000 duk wata don amfana da sabon tsarin wutar lantarki mai amfani da hasken rana
Kimanin yan Nijeriya miliyan 25 da aka shirya za su ci gajiyar tsarin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a duk faɗin ƙauyukan karkarar ƙasar wanda ake sa ran za su ringa biyan N4,000 kowane wata.
Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za ta fara girka aikin hasken rana na Naira biliyan 140 ga iyalai miliyan 5 a yankunan marasa galihu da na karkara daga makon farko na Disamba.
Gwamnatin tarayya ta lura cewa wannan shirin ci gaba ne na aiwatar da tsarin tattalin arzikin dorewa (ESP) na gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Hukumar wutar lantarki ta karkara (REA) ce ta aiwatar da wannan shirin.
A wata sanarwa a ranar Lahadi, Laolu Akande, babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya ce wadanda za su ci gajiyar...