
Za a yi wa Ali Nuhu da ‘yan Kannywood 5 gwajin coronavirus
Tauraron fina-finan Kannywood Ali Nuhu ya ce hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta Najeriya za ta yi masa gwajin cutar coronavirus.
Ali Nuhu da wasu 'yan Kannywood biyar na cikin taurarin da suka halarci bikin karrama jarumai da aka gudanar a Lagos ranar Asabar 14 ga watan Maris.
Gwamnatin jihar ta Lagos ta yi kira ga duk wanda ya halarci bikin ya je a yi masa gwajin coronavirus saboda ta gano cewa wani mai dauke da cutar ya halarci bikin.
Za a samu sakamako ranar Laraba
A hirar da ya yi da BBC ranar Talata da daddare, Ali Nuhu, ya ce jami'an hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta Najeriya sun je wurinsa inda suka bukaci ya bi su ofishinsu domin yi masa gwajin cutar ta coronavirus.
Kazalika ya ce su...