
Yaren Hausa ya zo na daya a gasar Rubutu inda Turanci yazo na 2
Wata gasar Rubutu da Kamfanin Wikimedia ya saka a ta bayyana sakamakon da aka samu inda yaren Hausa yazo na 1.
An samu rubutu da yaren Hausa da aka yi na mata har guda 179 inda Turanci ya zo na 2 da yawan 136.
Shugaban Wikimedia na Najeriya, Olushola Olaniyan ya yabbatar da hakan a ranar Litinin a Legas. Sauran yarukan dake takewa Hausa baya sune na kasar Indonesia sai na Yarbanci sai Inyamuranci