
Rikicin Saka Hijabi: Bidiyon yanda matasa suka rushe Masallacin dake cikin makaranta a jihar Kwara
Rikicin saka Hijabin dalibai a jihar Kwara na ci gaba da daukar wani sabon Salo inda Rahotanni na baya-bayannan na cewa wasu fusatattun matasa sun je makarantar Bishop Smith Secondary school inda suka rushe masallacin dake ciki.
Lamarin ya farune da duku-dukun yau Talata amma ba'a kai ga sanin ko su wanene suka rushe masallacin ba.
Wani Rahoton kuma yace, mahukuntar Makarantar sun tilastawa dalibai mata cire hijabansu kamin daga baya aka turasu gida.
Matasa dai sun shiga cikin makarantar suka kulle da hana dalibai da malamai shiga inda har suka hadawa kofar shiga Makarantar Shokin din wutar Lantarki, amma daga baya an yi sulhu dasu sun bude, kamar yanda Daily Post ta ruwaito.
Kalli Bidiyon a nan