
Hisbah ta kama mabarata 178 a jihar Kano
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wasu mutane 178 da ake zargi a cikin garin Kano saboda karya dokar hana bara a kan titi daga Satumba zuwa Nuwamba 2020.
Babban kwamandan hukumar, Mista Haroun Ibn-Sina, ne ya fadi hakan a Kano ranar Litinin.
“An cafke wadanda ake zargin ne a hanyar Alu Avenue, Dan’agundi, Taludu, Race Course, Sharada, Kofar Mazugal a cikin garin.
“Daga cikin wadanda aka kama 102 mata ne, yayin da 76 maza.
“Hukumar za ta ci gaba da cafke mabaratan da suka ki bin doka.