fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Hisbah kano

Hukumar Hisbah zata tsaurara matakai kan masu shan taba a gidan kallon Ball a jihar Kano

Hukumar Hisbah zata tsaurara matakai kan masu shan taba a gidan kallon Ball a jihar Kano

Tsaro
Hukumar Hisbah ta jihar KANO ('yan sandan Sharia), a ranar Laraba, tare da hadin gwiwar masu cibiyoyin taro a Kano za su tura jami'ansu domin sanya ido da kame masu halaye marar kyau a cibiyoyin. An cimma yarjejeniyar ne tsakanin shugabannin cibiyoyin taron da gidajen cin abinci a wani taro, wanda aka yi tare da Babban-Kwamanda, Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina. Wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na hukumar ta Hisbah, Lawan Fagge ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa ma'aikatan za su sa ido kan cibiyoyin kallon kwallon kafa, don hana shan sigari ba kakkautawa, da sauransu. Bayan haka, kwamitin zai kuma hana matasa shan shi-sha (wiwi da kayan maye) a cikin cibiyoyin.
Hukumar Hisbah ta Kano ta kama mutane 43 saboda karuwanci da sayar da giya

Hukumar Hisbah ta Kano ta kama mutane 43 saboda karuwanci da sayar da giya

Uncategorized
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wasu mutane 43 bisa laifin yin karuwanci da kuma sayar da giya ba bisa ka'ida ba a kasuwar kayan lambu ta Kwanar Gafan da ke karamar hukumar Garun Malam. Dokta Harun Ibn-Syna, Babban Kwamandan Hisbah wanda ya gabatar da wadanda ake zargin a ranar Litinin a unguwar Sharada, ya tabbatar da kamun.   Daga cikin 43, 34 mata ne yayin da ragowar tara kuma maza ne, masu shekaru tsakanin 15 zuwa 18.   Ya ce 14 sun kamu da cutar kanjamau, 10 sun san halin da suke ciki yayin da hudu ba su sani ba, sannan kuma an gano wasu kuli-kuli uku, da kwararon roba na maza da mata a kasuwar.   Ya ce anyi kamun ne tsakanin hukumar Hisbah da kuma hukumar hana fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya.
Da Duminsa: Hukumar Hisbah ta jihar Kano za ta hana yin ‘fati’ da bukukuwa da daddare saboda cin karo da lokacin Sallah

Da Duminsa: Hukumar Hisbah ta jihar Kano za ta hana yin ‘fati’ da bukukuwa da daddare saboda cin karo da lokacin Sallah

Tsaro
Hukumar Hisba ta ce tana shirin hana yin bukukuwa da daddare musamman ma ‘fati’ a fadin jihar Kano, sakamakon cin karo da lokutan Sallah da galibin bukuwan ke yi.   Babban kwamandan hisba na jihar Kano Muhammad Harun Sani Ibn Sina ne ya bayyana hakan ya yin ganawarsa da manema labarai a Kano. Ibn Sina ya ce galibin ‘yan mata da suke yin biki musamman ma masu yi fatin dare na mancewa da yin sallar Magriba da kuma ta Isha’I ciki kuwa harda Amarya.   Ya ce babban abin takaicin ma shi ne galibin wuraren da ake bukuwan wurare ne da ake shan shisha da aikata al’amura marassa dadi, da masu bikin ke fakewa da shi suna barna.   “ Wanann yana tayar min da hankali, saboda yadda yaran mu da kannemu ke rayuwar abin takaici.   “Wanna abun sai dai a ce i...
Hotunan yanda Hisbah ta yi binciken Daki-Daki dan gano masu ayyukan Ashsha

Hotunan yanda Hisbah ta yi binciken Daki-Daki dan gano masu ayyukan Ashsha

Uncategorized
Rahotanni daga jihar Kano na cewa Hukumar Hisbah dake jihar ta gudanar da bincike daki-daki dan neman masu aikata ayyukan ashsha.   Rahoton wanda Sahara Reporters ta samar ya bayyana cewa Hisbah ta yi wannan bincike ne a jiya, Juma'a, 27 ga watan Nuwamba. Tace wani wajan Shakatawa me suna Hill and Valley dake Dawakin Kudu inda ma'aikatan wajan suka zagaya da hukumar dan ganin yanda lamura ke gudana.   Rahoton dai ya jawo cece-kuce sosai a shafukan sada zumunta.
Ina rokon ku daina Askewa matasa gashi, Tara Suma ba laifi bane>>Sanata Shehu Sani ga Hisbah ta Kano

Ina rokon ku daina Askewa matasa gashi, Tara Suma ba laifi bane>>Sanata Shehu Sani ga Hisbah ta Kano

Siyasa
Da safiyar yau ne aka tashi da labarin cewa hukumar Hisbah dake Kano ta fara askewa matasa masu tara suma gashi.   Hotunan hakan sun watsu sosai a shafukan sada zumunta inda suka jawo cece-kuce.   Sanata Shehu Sani wanda ake wa lakabin me Gashi ya jawo hankalin Hisbah da cewa su daina Askewa matasan Gashi saboda tara sumar ba laifi bane. Yace zai yi magana da matasan su rika kula da gashin nasu. https://twitter.com/ShehuSani/status/1312755678885425153?s=19   Sanata Sani ya bayyana hakane a shafinsa na Twitter. "Dear Hisbah, I appeal to you to stop shaving the Hairs of those young men.Abundance hair is not a Crime.Its Our natural identity.I will talk to them to dress it well. Thank you"
Hukumar Hisbah A Jihar Kano ta Sha Al’washin Yiwa Masu Yin Askin Banza Aski

Hukumar Hisbah A Jihar Kano ta Sha Al’washin Yiwa Masu Yin Askin Banza Aski

Uncategorized
Shugaban Hukumar Hisba Dake Jihar Kano, Harun Ibn Sina yayi gargadin cewa duk wanda hukumar tai Ido biyu dashi dauke da Askin banza toh lashakka hukumar zata cafke shi kuma tai masa kwal kwabo. Shugaban yayi wannan kiran ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a jihar. Harun Ibn Sina ya kuma yi kira da masu tallan gomaka a jihar da su ji tsoran Allah su daina, inda ya bayyana cewa hukumar hisba a jihar Kano, na samun korafe-korafe na yadda wasu mutane ke a jiye gomaka a cikin shagunan su Wanda A cewarsa hakan ya saba da al'adar al'ummar jihar. Haka zalika ya ce, hukumar za tai duk mai yuwa wajan yiwa masu wannan dabi'a nasihohi ta hanyoyin da su ka dace, amma ya sha al'washin cewa duk wanda yayi kunnan kashi toh hakika hukumar zata dauki mataki a kan sa.
Hukumar Hisbah dake jihar kano ta gabatar da rabon kudade ga masu jiran makabartu a jahar

Hukumar Hisbah dake jihar kano ta gabatar da rabon kudade ga masu jiran makabartu a jahar

Tsaro
Shugabancin Hukumar Hisbah ta jihar Kano tare da hadin gwiwar manyan ma'aikatun Shari'a, da Hukumomi a jihar sun kai ziyarar ban girma ga makabartu guda 5 dake cikin birnin jahar kano tare da baiwa masu gadin makabartun dubunnan kudade. Dayake magana a lokacin da ya ke gabatar da kudaden Sugban hukumar hisba Sheik Haruna Muhammad Ibn Sina ya bayyana cewa hukumar ta shirya wannan ziyarar ne bisa la’akari da namijn kokarin da masu aikin sa kai dake makabartun keyi wanda ya zama wajubi a girmama su. Makabartun da hukumar ta ziyarta sun hada da makabartar fam santa, da makabartar Tarauni, Dan Dolo a Gwale, Kara ko kofar mazugal, Tudun Murtala, da  Gama, a Nassarawa.