
An damke wani matashi da yake sojan gona Ya na cewa shi mace ce
Jami'an kukumar Hisba ta jihar Kano sun kama matashin Mai suna Usman A. Usman Wanda yace sunansa Amina Kuma yace shi ya zo ne daga Zariya.
Matashin dai ya kutsa kai a ofishin hukumar Hisba Inda yace yana neman ayi masa garanto a wajan wani aikin gidan abinci, nan take wani jami'in Hisba yace bai Yadda da shi ba Koda aka matsa bincike shine Aka gano garjejan namijine.
A halin da ake ciki dai Yana hannun hukumar domin amsa tambayoyi.