fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Tag: Hisbah

Hisbah ta hana ‘yan mata rike babbar waya a kauyen Kuriga dake Jihar Kaduna

Hisbah ta hana ‘yan mata rike babbar waya a kauyen Kuriga dake Jihar Kaduna

Siyasa
Hisbah a kauyen Kuriga dake karamar hukumar Chukun na jihar Kaduna ta hana mata rike waya kamar yanda Rahotanni suka bayyana.   A hirar da wasu mazauna garin suka yi da Sahara Reporters sun bayyana cewa dokokin da Hisbar take sakawa a garin na hansu rawar gaban hantsi. Wani mazaunin garin yace Hisbah ta hana 'yan mata rike babbar waya da da ikirarin cewa ana amfani da ita wajan bata tarbiyyarsu.   Hakanan Hisbah tana hana matan saka irin katoton gisal dinnan.   Wani kuma cewa yayi har cikin gida jami'an Hisbah ke shiga a garin suna kama mutane idan ana shagalin biki.   "Hisbah had been ‘frustrating the lives of youths in Kuriga and often carry out severe punishment for moral failings’. “Hisbah is punishing youths for keeping afro hair a...
Hukumar Hisbah ta gano wani laifi da zai iya jawo a daure wanda aka samu da aikata shi har tsawon shekaru goma a gidan kaso, wanda yawancin matasa suka raja’a a kan sa

Hukumar Hisbah ta gano wani laifi da zai iya jawo a daure wanda aka samu da aikata shi har tsawon shekaru goma a gidan kaso, wanda yawancin matasa suka raja’a a kan sa

Tsaro
Daurin Shekaru 10 Da Matasa Suke Yayinsa hattara Iyaye Hukumar Hisbah ta gano wani laifi da zai iya jawo a daure wanda aka samu da aikata shi har tsawon shekaru goma a gidan kaso, wanda yawancin matasa suka raja'a a kan sa. Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah Mai lura da sashen Nazarin aikata manyan laifuka, Mallam Idris Ibn Umar, Shine ya shaida mana wannan laifin. Mallam Idris, ya bayyana cewa idan aka duba dokar "Panel Code" Boye dan Adam yana jawo a daure mutum har tsawon shekaru goma. Ya ce, yanzu matsalar da Hisbah take samu a bangarensa shine matashi ya boye yarinya a dakin kwanansa, har tsawon kwanaki ko mako guda iyayenta suna ta nemanta, basu san tana can tana kwana da Namiji ba. Mataimakin na babban kwamanda, ya ce, Dole ne hukumar Hisbah ta fadakar da al'ummar ung...
Hisbah ta kama karamin Yaro masoyin Ado Gwanja

Hisbah ta kama karamin Yaro masoyin Ado Gwanja

Nishaɗi
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wani kankanin yaro mai suna Abdullahi Muhammad dan asalin karamar hukumar Shelang ta jihar Adamawa, wanda ya zo Kano domin haduwa da fitaccen mawakin nan Ado Isa Gwanja.   Abdullahi Muhammad mai shekaru goma ya biyo motar gawayi daga garin Shelang har zuwa nan Kano, ba tare da sanin iyayen sa ba.   Wakilin mu Yusuf Ali Abdallah ya rawaito mana cewa, jami’an Hisba sun dakume yaron kafin ya samu ganawa da Ado Gwanja.   Gwani Murtala Mahmud shi ne kwamandan Hisbah na karamar hukumar Kumbotso ya ce, yanzu haka suna shirye-shirye domin mayar da wannan yaron zuwa ga hannun iyayen sa.   Ku kasance da shirin Inda Ranka @7am don jin yadda wannan yaro ya rerawa shirin Inda Ranka wata wakar sa.
Hukumar hisba ta jihar kano ta gano maganin cutar coronavirus

Hukumar hisba ta jihar kano ta gano maganin cutar coronavirus

Uncategorized
Hukumar hisba ta Jihar kano tace ta gano maganin cutar corona da ta addabi duniya.   Babban kwamandan hukumar shiekh Haroun Ibn Sina ne ya bayyana hakan ta cikin wani sauti da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya litinin.   Ibn Sina yace "Babban maganin cutar Coronavirus shine komawa ga Allah ta hanyar neman gafara da yawaita istigfar da bin Allah sau dakafa.   Haka zalika kwamandan yace "Abinda ya jawo wannan cuta shine yawan sabon Allah da kuma rashin bin dokokin Allah da al'umma basayi.   Sannan shiek ibn sina ya kara da Jan hankalin mutane kan suyi watsi da duk wasu bayanai na jita jita da ake yadawa kan suyi amfani da tafarnuwa ko albasa wai dan maganin cutar coronavirus.   Rahotan da Hutudole ya tattara ya gano cewa tun bayan...