
Manyan jami’an hukumar Kwastam na fuskantar tuhumar karyar Shekaru
Hukumar Kwastam dake hana fasakwaurin kayayyaki zuwa cikin Najeriya na tuhumar wani babban jani'inta, DCG Chidi Augustine bisa zargin Almundahana da karyar shekaru.
Yayi amfani da lambar wani da ya mutu inda ya canja shekarunshi dan kada a masa ritaya da wuri. Sannan kuma ya canja jiharsa daga Delta zuwa Abia da kuma kwace gurbin aikin Kudu Maso kudu dan dai Almundahana.
Wannan kadanne daga cikin laifukan da ake zarginshu dasu.
Shugaban hukumar, Hamid Ali ya bayar da umarnin yin bincike akan Chidi dama wasu sauran manyan jami'an hukumar da suke da irin wannan laifi.
Idan dai aka samesu da laifi a binciken da ake to za'a kori da yawa daga cikinsu. Vanguard ta bayyana cewa da yawan mananan ma'aikatan hukumar na murna da wannan bincike da akewa Ch...