
Kalli bidiyon Mawakin kudu, Dbanj yana rawa da wakar Hamisu Breaker ta Jarumar Mata
Ga dukkan alamu wakar tauraron mawakin Hausa, Hamisu Breaker ta Jarumar Mata bata gama tashe ba, bayan matan aure sun rikawa mazajensu rawa da ita a lokacin kullen Coronavirus/COVID-19 da aka yi.
A wannan karin kuma mawakin kudancin Najeriya, Dbanj ne yayi rawa da wakar ta Jarumar mata inda yace Hamisun ya kirashi da gaggawa dan wakarshi ta birgeshi.
https://www.instagram.com/p/CEaJ78cJdvM/?igshid=1lqi3wwl2qq2y
Hamisu ya amsa inda ya bayyana cewa to zan kiraka Maza Maza. Ga dukkan alamu bidiyon ya fitone daga tauraruwar fina-finan Hausa,Maryam Booth.