
Jami’an gidan yari, da masu babura sun yi arangama a Ibadan
Anyi wata hantsaniya a yankin kofar Agodi da ke Ibadan biyo bayan wani rikici da ya barke tsakanin wasu masu baburan hawa da jami’an gidan yarin Agodi dake Ibadan.
Har yanzu ba a iya gano musabbabin fadan ba, wanda ya fara tun safiyar Talata, amma wakilin jarida PUNCH ya samu rahoton cewa an harbe mutum biyu.