fbpx
Friday, May 27
Shadow

Tag: Ibrahim Boubacar Keita

An garzaya da hambararren shugaban kasar Mali UAE dan Neman Lafiya

An garzaya da hambararren shugaban kasar Mali UAE dan Neman Lafiya

Siyasa, Uncategorized
Rahotanni daga kasar Mali na cewa an garzaya da tsohon shugaban kasar da Sojoji suka hambarar a juyin Mulki, Ibrahim Boubacar Keita zuwa kasar UAE dan neman Lafiya.   Keita ya samu rakiyar Matarsa, Amina sa wasu likitoci da jami'an tsro. Kamfanin dillancin labaran AP ya bayyana cewa da yammavin Yau, Asabar ne aka tafi da tsohon shugaban zuwa UAE. A baya dai mun ji cewa an garzaya da tsohon shugaban kasar Asibiti a Mali bayan da ciwon mutuwar barin jiki ta kamashi.   A wani Labari me dangantaka da wannan kuma Rahotanni daga kasar na cewa sojojin masar 2 ne aka kashe a wani hari.
Yanzu-Yanzu:Ciwon mutuwar barin jiki ya kama hambararren shugaban kasar Mali

Yanzu-Yanzu:Ciwon mutuwar barin jiki ya kama hambararren shugaban kasar Mali

Siyasa, Uncategorized
Rahotanni daga kasar Mali na cewa ciwon mutuwar rabin jiki ta kama hambararren shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita.   Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayyana cewa likitan Shugaban ya gaya musu ciwon ba mai tsanani bane amma alamace dake nuna cewa nan gaba me tsananin zai iya kama shugaban. A baya dai wani hadimin shugaban ya bayyana cewa an kwantar dashi a Asibiti kuma za'a sallameshi a yau dan kawai ya je a duba lafiyarsa ne amma daga baya kuma sai aka bayyana cewa za'a ci gaba da dubashi har abinda hali yayi.   Sojojin da suka hambarar dashi dai sun bayyana cewa idan akwai bukatar ya fita kasar waje neman lafiya zasu bashi damar hakan.
An kwantar da tsohon shugaban Mali Keita a asibiti

An kwantar da tsohon shugaban Mali Keita a asibiti

Siyasa
Rahotanni daga Mali na cewa an kwantar da hambararren shugaban kasar a asibiti. Kamfanin dillacin labarai na Associated Press ya ambato majiyoyi biyu daga asibiti na cewa tsohon shugaban kasar yana samun kulawa. An hambarar da Ibrahim Boubakar Keita mai shekara 75 daga kan mulki ne makonni biyu da suka wuce sannan kuma aka tsare shi na tsawon kwana goma a wani sansanin soji kafin a ba shi damar walwala. Lokacin da ake gudanar da tattaunawar sulhu, Mr Keita ya ce ba ya son komawa kan mulki. 'Yan hamayya sun kwashe watanni suna kira a gare shi ya sauka daga mulki, inda suka dora alhakin tabarbarewar tattalin arziki da tsaro, da kuma cin hanci da rashawa a kansa.
Abinda ya faru a Mali ya dameni sosai, ya kamata a kakabawa sojojin da suka kwace mulkin takunkumi>>Shugaba Buhari

Abinda ya faru a Mali ya dameni sosai, ya kamata a kakabawa sojojin da suka kwace mulkin takunkumi>>Shugaba Buhari

Siyasa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa juyun mulkin da ya faru a kasar Mali ya dameshi sosai inda yayi kira da a sako shugaban kasar, Ibrahim Boubacar Keita da membobin gwamnatinsa da aka kama.   Shugaban kasar ya bayyana hakane a zaman ganawar da aka yi tsakanin kasashen Membobin ECOWAS a jiya, Alhamis. Hutudole ya kawo muku Yanda aka yi zaman ganawar a jiya inda shugaba Buhari ya halarta ta kafar sadarwar zamabi daga Abuja. Shugaban yac koda murabus din da shugaba Keita yace yayi, tursasa masa aka yi dan haka ya kamata a hada kai a kakabawa sojojin da suka yi juyin mulkin takunkumi dan hakan yasa su mayarwa da shugaban kasar Mukaminsa.   Za'a aika tsohon shugaban kasar Najeriya,  Goodluck Jonathan da Jean Claude su kaiwa sojojin kasar Malin sakon mat...