
Zakzaky ya bayar da gudummawar magunguna, gidan sauro, ga ‘yan gudin Hijira A Jihar Katsina
A ranar Talata ne jagoran Shi'a Sheikh Ibrahim Zakzaky ya bayar da gudummawar magunguna da kuma gidajan sauro ga 'yan gudun hijira dake a karamar hukumar Faskari a jihar Katsina,
Wakilin Zakzaky Rabi'u Abdullahi ya bayyana cewa, an zabi Faskari ne dake jihar domin bayar da gudunmawar ga 'yan gudun hijirar da suka bar garuruwansu saboda fargabar kai hari daga ‘yan bindiga.
Abdullahi sannan ya kara da cewa shugaban da aka tsare zai ci gaba da taimaka wa mutane, musamman a wannan mawuyacin lokaci.
A karshe Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta saki jagoran kungiyar tasu.