
Da dumi-dumi: Gwamnatin Kano Za ta fara kamen wadanda ba sa sanya ‘Face Mask’
Daga Ibrahim Hamisu Kano
Gwamnatin jihar Kano za ta fara kamen wadanda ke yawo ba tare da sanya takunkumin fuska ba wato (Face Mask) daga Laraba mai zuwa.
Jaridar Hutudole ta ruwaito dawo da dokar sanya takunkumin ya biyo bayan sake barkewar cutar ‘Kwarona’ a jihar Kano dama kasa baki daya.
mashawarci na musamman kan kafafene sadarwa na zamani ga gwamnan Kano Salihu Tanko Yakasai, ya ce dokar dama ba sabuwa bace, kuma gwamnati ba ta ce ta janye ba, jama’a ne suka daina sakawa.
Ya ce ya dole a dowa da dokar, idan akai laakari da yadda annobar ta sake kunno kai, domin a kubutar da jama’a da ga hadarin kamuwa da cutar da kuma yadawa jama’a.
Salihu Tanko Yakasai ya kara da cewa ya zama wajibi ko wanne dan jihar Kano ya zama yana yawo da takunkum...