fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Ibrahim Kasimu Obashi

‘Abin da ya ba ni karfin gwiwar in auri mata biyu a rana guda>>ango Ibrahim Kasimu Oboshi

‘Abin da ya ba ni karfin gwiwar in auri mata biyu a rana guda>>ango Ibrahim Kasimu Oboshi

Auratayya
Wani manomi dan shekaru 35 da haihuwa kuma mai wakiltar mazabar Iwogu a karamar hukumar Keana ta jihar Nasarawa, Ibrahim Kasimu Oboshi, wanda aka fi sani da Ogah, ya auri wasu mata biyu a rana daya. Ya auri Nazira Dahiru Ozegya da Rabi Isyaku Akose a ranar 28 ga Maris, 2020. A lokacin da yake Magana da jaridar Daily Trust a ranar Asabar, ya ce, “Ni maraya ne, mai yin noma kuma a yanzu ni kansila ne. A matsayina na maraya, na ɗauki noma da makaranta da muhimmanci, da harkar noma ne, na sami damar kula da mahaifiyata da kaina. Daga baya ne, na ci zabe don wakiltar garina. ”   Ya ce lokacin da mutane da yawa suka ji yana shirin auran mata biyu, sai suka yi mamaki ko shi ɗan sarki ne ko ɗan wani attajiri ne, amma an gaya musu cewa ni manomi ne. "A gaskiya na rike noma da matu...