fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Ibrahim Magu

Na kadu da nadin sabon Shugaban EFCC>>Ibrahim Magu

Na kadu da nadin sabon Shugaban EFCC>>Ibrahim Magu

Siyasa
Tsohon Shugaban hukumar yaki da rashawa, EFCC, Ibrahim Magu yayi martani ga sabon nadin da shugaba Buhari yayi na sabon shugaban hukumar.   Lauyan Magu, Tosin Ajaomo ya bayyana cewa lamari  ya kadasu matuka.   Shugaba Buhari ya nada Abdulrasheed Bawa dan shekaru 40 mukamin sabon Shugaban EFCC inda ya aikewa Majalisa da neman ta amince masa da nadin.   Lauyan na Magu yace kamata yayi a gama binciken da akewa wanda yake aiki kamin a ci gaba da maganar wani mataki na gaba.   “Sincerely, I need to tell you that this appointment came to me as a shock. There is still an unfinished assignment that was pending,” he said. “I was expecting that the issue of Magu would have been sorted out before moving to another stage. “Unfortunately, we just got th...
Be kamata sabon Shugaban EFCC na Gaba ya fito daga bangaren yan sanda ba>>Mai Shari’a Salami

Be kamata sabon Shugaban EFCC na Gaba ya fito daga bangaren yan sanda ba>>Mai Shari’a Salami

Siyasa
Justice Ayo Salami, shugaban kwamitin da aka kafa domin binciken zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yiwa Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Ibrahim Magu, ya ba da shawarar cewa be kamata sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ya fito daga rundunar ‘yan sanda. Ya bayar da wannan shawarar ne a ranar Juma’a, bayan ya gabatar wa da Shugaba Muhammadu Buhari rahoton kwamitin da aka kafa don binciken zargin cin hanci da rashawa da Babban Lauyan nan kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, keyi akan shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu.   A cewarsa, shugabannin hukumar EFCC hudu da suka gabata sun fito ne daga rundunar 'yan sanda ne, don haka ya kamata a ba da dama ga mutane daga wasu jami'an tsaro ko jami...
Akwai Rashawa a duk matakai na Gwamnati amma ina son Duniya ta ga Najeriya a matsayin kasar da bata yadda da Rashawar ba>>Shugaba Buhari

Akwai Rashawa a duk matakai na Gwamnati amma ina son Duniya ta ga Najeriya a matsayin kasar da bata yadda da Rashawar ba>>Shugaba Buhari

Siyasa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa burinsa shine Duniya ya zamana tanawa Najeriya kallon kasar da bata yadda da rashawa da cin hanci ba.   Ya bayyana hakane a fadarsa, Abuja yayin da yake karbar Rahoton binciken da akawa dakataccen mukaddashin shugaban hukumar EFCC,  Ibrahim Magu.   Yace babu kasar da babu cin hanci saidai wata kasar na yakarsa da gaske yayin da wata kasar kuma ke wa yaki da rashawa da cin hanci rikon sakwa-sakwa.   Yace a kowane mataki na Gwamnati da al'amuran mu akwai rashawa da cin hanci amma yana son yayi yaki da ita ta yanda Duniya zata ga cewa Najeriya bata yadda da cin hanci da Rashawa ba.   Shugaba Buhati yace ya kawo tsare-tsare irin su TSA da BVN da sauransu da yaki da rashawa. Sannan kuma yace babu wanda y...
Da Duminsa: Yanzu haka Shugaba Buhari na karbar Rahoton Binciken da akawa Magu

Da Duminsa: Yanzu haka Shugaba Buhari na karbar Rahoton Binciken da akawa Magu

Siyasa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a yanzu haka yana karbar Rahoto akan binciken da akawa dakataccen mukaddashin shugaban hukumar EFCC,  Ibrahim Magu.   Shugaban na karbar wannan Rahoto ne a fadarsa daga kwamitin Mai shari'a Ayo Salami. Shafin fadar shugaban kasa, Presidency Nigeria ne ya bayyana haka. https://twitter.com/NGRPresident/status/1329726818262396928?s=19 NOW: President @MBuhari receiving the report of the Judicial Commission of Inquiry on the Investigation of Mr. Ibrahim Magu, the Acting Chairman, @officialEFCC. Justice Ayo Salami, Chair of the Judicial Commission, presenting the Report. #AsoVillaToday
Juma’a Me zuwa za’a mikawa Shugaba Buhari sakamakon Binciken da aka yi akan Magu

Juma’a Me zuwa za’a mikawa Shugaba Buhari sakamakon Binciken da aka yi akan Magu

Tsaro
Rahotanni daga fadar shugaban kasa, Kwamitin Mai Shari'a Ayo Salami dakw binciken dakataccen mukaddashin shugaban EFCC,  Ibrahim Magu na cewa Juma'arnan me zuwa za'a mikawa shugaba Buhari sakamakon binciken.   Wata Majiya a wajan Binciken ta tabbatarwa da Premium times haka. Kuma kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu shima ya tabbatar da wannan lamari. He said, “Yes I can confirm the panel would be submitting its report to the president on Friday.”
Wata Sabuwa: Kotun da’ar Ma’aikata ta gayyaci Magu kan zargin karyar Kadarorin da ya mallaka

Wata Sabuwa: Kotun da’ar Ma’aikata ta gayyaci Magu kan zargin karyar Kadarorin da ya mallaka

Siyasa
Kotun da'ar ma'aikata da ake kira da CCB ta aikewa  da dakataccen mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu da sammace.   Kotun ta bukaci Magu ya bayyana a gabanta da takardun duka kadarorin da ya mallaka tun bayan fara aikinsa a matsayin jami'in Gwamnati.   Peoplesgazette ta bayyana cewa ta gano takardar gayyatar da aka masa. Hakan na zuwane yayin da akewa Magu binciken aikata ba daidai ba karkashin kwamitin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar.
Na yi dana sanin shugabantar binciken Magu>>Mai Shari’a Ayo Salami

Na yi dana sanin shugabantar binciken Magu>>Mai Shari’a Ayo Salami

Siyasa, Uncategorized
Mai shari'a, Ayo Salami wanda tsohon shugaban babbar kotun gwamnatin tarayya ne ya bayyana cewa yayi nadamar shugabantar Binciken Dakataccen mukaddashin shugaban hukumar, EFCC, Ibrahim Magu.   An hana 'yan Jarida shiga wajan da ake binciken inda kuma Magu ya fara kare kansa daga zarge-zargen da ake masa. Wasu lauyoyin magu 2, Zainab Abiola da Tosin Ajaoma sun bayyanawa Premium times cewa Mai Shari'a, Salami ya yi ta maimaita cewa yayi dana sanin shugabantar Binciken Magu.   Yace yana can gida zaune yana cin tuwo tun bayan da yayi rutaya amma yanzu ya zo ya saka kanshi a wannan bincike. Saidai da lauyoyin suka tambayeshi ko saboda an kasa samun Magu da laifine shiyasa yace haka?  Bai basu amsa ba.
Tunda nike ban taba karbar Cin hanci ba>>Magu

Tunda nike ban taba karbar Cin hanci ba>>Magu

Siyasa, Uncategorized
Dakataccen mukaddashin shugaban EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana cewa tunda yake bai taba karbar cin hanci ba.   Ya bayyana hakane jiya, Laraba a gaban kwamitin Mai Shari'a Ayo Salami dake bincikensa akan zargin aikata ba daidai ba. Magu ya bayyana hakane yayin da yake karyata zargin da aka masa na taimakawa wata mata, 'yar kasar Nijar, Hima Aboubakar ta tserewa shari'a, yace idan akwai wanda ya taba bashi cin hanci to ya fito ya fada.   Tun a ranar Litinin din data gabatane, Magu ya fito dan kare kansa daga zarge-zargen da ake masa.
Ministan Shari’a ya ki amsa gayyatar da kwamitin dake binciken Magu ya masa

Ministan Shari’a ya ki amsa gayyatar da kwamitin dake binciken Magu ya masa

Siyasa
Ministan Shari'a, Abubakar Malami ya ki amsa gayyatar da kwamitin Ayo Salami dake binciken, zargin aikata ba daidai ba da ake wa mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu.   Kwamitin ya gayyaci Malami ne bayan da Magu yayi korafin cewa ya kamata Malamin da yake masa zargin aikata ba daidai ba ya bayyana dan kare zargin da ya masa. Hakanan Magu ya kuma bukaci da a sako dawo da duk wani shaida da ya bayar da shaida akan shari'ar tasa inda yace ba'a bashi damar ganawa da shaidun ba.   Saidai Malami a martaninsa, kamar yanda Sahara Reporters ta samo yace ba zai bayyana a matsayin shaida ba akan zargin da akewa Magu, saidai idan gayyatar a karkashin Umarnin shugaban kasa, Muhammadu Buhari dan girmama dokane.   Ya kuma bayyana cewa, zargin da yawa Ma...
An zargi shugaban Kwamitin dake Bincikar Magu, Ayo Salami da son ci gaba da karbar Miliyoyin Alawus shiyasa baya so binciken ya kare

An zargi shugaban Kwamitin dake Bincikar Magu, Ayo Salami da son ci gaba da karbar Miliyoyin Alawus shiyasa baya so binciken ya kare

Uncategorized
Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin Mai shari'a Ayo Salami wanda shine ke jagorantar kwamitin dake binciken tsohon Mukaddashin shugaban hukumar EFCC,  Ibrahim Magu da ci gaba da neman a tsayawaitawa kwamitin nasa lokacin aiki saboda ya ci gaba da karbar Miliyoyin Alawus da yake samu daga aikin. Kafar Sahara Reporters tace tuni shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amince da tsawaita aikin kwamitin binciken da makwanni 6. Saidai tace maimakon tunanin aiki ne ya ma kwamitin yawa kwamitin yawa, maganar gaskiya itace son ci gaba da karbar Manyan alawus ne na shugaban kwamitin kamar yanda wata Majiya ta bayyana.   Majiyar ta yi zargin cewa a duk zaman da kwamitin yayi ana biyan mai shari'a Ayo Salami Naira Dubu 250 da kuwa sauran wasu alawus da ba'a son bayyanawa.   ...