
Tsohon Gwamnan Jihar Katsina Shema Yayi Kira Da Hadin Kai Tsakanin Hukumomin Tsaro
Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema ya yi kira da a hada karfi da karfe tsakanin hukumomin tsaro domin magance matsalar rashin tsaro da kasar ke fuskanta.
A cewarsa, dole ne hukumomin tsaro su daina daukar kansu a matsayin abokan hamayya, sannan kuma dole ne ‘yan kasa su bayar da nasu kason tare da karfafawa shugabanninsu gwiwa don yin abubuwan da suka dace domin maido da zaman lafiya da daidaito a kasar.
Shema ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin kaddamar da Kwamitin Taro da na Dattawan Jiha a Hedikwatar Jam’iyyar PDP ta Jihar Katsina, a karshen mako.
Shugaban jam'iyyar na jihar, Salisu Majigiri a wajen taron ya shaida wa manema labarai cewa ta wannan kaddamarwar, an gama jam'iyyar tare da dukkanin gabobi 20 da Kundin tsarin mulkin jam'iyyar ...