
Ban yadda da cewa Shekau zai mika Wuya ba kuma ana Amfani da tsaffin hotuna dan nuna cewa Sojoji na nasara akan Boko Haram >>Audu Bulama Bukarti
A ‘yan kwanakin nan ana ta rade-radin cewa jagoran Boko Haram, Abubakar Shekau yana so ya mika wuya ga mahukuntan Najeriya.
A lokacin da Babban jami’in cibiyar samar da bayanai a hedikwatar tsaron Najeriya, Manjo Janar John Enenche ke tofa albarkacin bakinsa kan lamarin, ya ce “muddin Shekau ya bi tsarin da ake bi a kasar nan wajen mika wuya, toh, tabbas za mu karbe shi.”
Shi ma kakakin sojojin Najeriya, Kanar Sagir Musa ya tabbatar da jin wannan jita-jitar.
“Muna da labarin cewa Shekau yana so ya mika wuya, amma wannan ba shi ke gabanmu ba, yakin da muke yi shi ya dame mu,” a cewar kakakin.
Sai dai tun da aka fara yada wannan jita-jitar mutane suka fara saka alamar tambaya kan lamarin.
 ...