
Kotu zata fara sauraren bukatar sallamar Zakzaky Saboda gwamnati ta kasa bada gamsashshiyar hujjar laifin da yayi
Nan da ranar 30 ga watan Yuli babbar Kotu a Kaduna zata fara sauraren bukatar Shugaban Kungiyar Shi'a, Sheikh Ibrahim Zakzaky kan a sallameshi tunda dai gwamnati ta kasa kawo hujja akansa.
Zakzaky zai gabatar da wannan bukatane ta hannun lauyansa, Femi Falana.
Kotun dai ta bukaci duka bangarorin 2 na wanda ake kara da wanda ke karar su gabatar da hujjoji akan juna.