fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Tag: Ibtila’i

Gobara a matsugunin ‘yan gudun hijira dake Borno ta kashe mutum 1 tare da raba mutane sama da Dubu 1 da matsuguninsu

Gobara a matsugunin ‘yan gudun hijira dake Borno ta kashe mutum 1 tare da raba mutane sama da Dubu 1 da matsuguninsu

Uncategorized
Rahotanni daga jihar Borno na cewa akalla mutum 1 ne ya rasu sanadiyyar gobarar data tashi a matsugunin 'yan gudun Hijira dake Borno. Lamarin ya farune a matsugunin Muna sanadiyyar wutar da ta tashi daga wani dakin dafa Abinci, kamar yanda hukumar bada Agajin gaggawa ta kasa, NEMA ta bayyana.   Hakanan gobarar ta raba mutane 1613 da matsugunin.   Kalli hotunan yanda Lamarin ya faru a kasa  
An damke yarinyar da ta luma wa mutumin da ya yi kokarin yi mata fyade wukar fere doya

An damke yarinyar da ta luma wa mutumin da ya yi kokarin yi mata fyade wukar fere doya

Uncategorized
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas Bala Elkana ya bayyana cewa sun damke wata yarinya mai shekaru 16 da aka kama da laifin kashe wani mutum mai suna Babatunde Ishola saboda danneta da ya nemi yi da karfin tsiya.   Elkana ya fadi haka ne ranar Lahadi inda ya kara da cewa wannan abin takaicin ya faru ne ranar Asabar a gidan mamacin dake zama a Ogundele Aboru jihar Legas.   Ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa Babatunde mai shekaru 44 na aikin gadi a makarantar sakandaren da wannan yarinya ke karatu kuma shi abokin mahaifin yarinyar ne.   Dama kuma Babatunde ya dade ba shi da mata, shi kadai yake zama a gidansa.   Ita dai wannan daliba kan garzaya gidan Babatunde ta na taya shi dan aikace-aikace kama share-share ne, wanke-wanke da saura...
Hadarin Mota Ya Halaka Mutane 23 A Jihar Jigawa

Hadarin Mota Ya Halaka Mutane 23 A Jihar Jigawa

Uncategorized
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN Kimanin mutane 23 ne suka rasu a yau Litinin sakamakon hadarin mota da ya rutsa da su a yankin Gwamfai dake karamar hukumar Jahun a jihar Jigawa.   Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Jigawa, Audu Jinjiri ne ya tabbatar da hakan, inda ya kara da cewa hadarin ya auku ne sakamakon fashewar tayar motar.   Jinjiri ya kara da cewa motar kirar Toyota mai rijistar lamba YD183 HDJ, tana dauke ne da fasinjoji daga karamar hukumar Jahun zuwa kasuwar Shuwarin dake karamar hukumar Kiyawa a yayin da lamarin ya auku.   'Yan sanda sun kuma bayyana sunan direban motar da Ayuba mai shekaru 36 dake kauyen Afasha a karamar hukumar Jahun.
Ya kashe Budurwarsa ‘yar shekaru 14 a Katsina bayan data zargeshi da Dirka mata cikin shege

Ya kashe Budurwarsa ‘yar shekaru 14 a Katsina bayan data zargeshi da Dirka mata cikin shege

Uncategorized
Wani Matashi me suna Shafi'u Haruna dan kimanin shekaru 27 ya kashe budurwarsa bayan da aka zargeshi da dirka mata cikin shege.   Shafi'u Haruna ya ja budurwarsa, Hamsiya Lawal 'yar kimanin shekaru 14 bayan garinsu, Dorawar Natiba dake garin Birdigau karamar hukumar Kankara inda ake zarginshi da amfani da wani murgujejen Dutse wajan fasa mata kai kuma ta mutu, kamar yanda kakakin 'yansandan jihar,SP Gambo Isah ya shedarwa manema labarai.   Haruna ya aikata laifinne a watan Disambar Shekarar 2019 data gabata amma ba'a samu kamashi ba sai ranar talatar makon daya gabata.    
Magidanci Da Matarsa Da ‘Ya’yansa Biyu Sun Rasu Bayan Da Motar Dangote Ta Buge Su A Kano

Magidanci Da Matarsa Da ‘Ya’yansa Biyu Sun Rasu Bayan Da Motar Dangote Ta Buge Su A Kano

Uncategorized
Wata motar siminitin Dangote ta hallaka mutane hudu a unguwar Gaida dake Kano.   Gidan Radion Freedom Kano ya rawaito cewa lamarin da ya faru ya rutsa ne da wani magidanci mai suna Muhammad Sagir mai shekaru 40 tare da matarsa da ‘ya’yansa uku wadanda suke tafiya akan babur lokacin da al’amarin ya faru.   Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa da faruwar al’amarin, inda ya ce 'yan sanda sun kwashi mutane biyar da hadarin ya rutsa da su zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad.   Sai dai magidancin da matarsa da ‘ya’yan sa biyu sun rasu, yayin da daya daga cikin ‘ya’yan mutumin ya tsira da ransa.   Kakakin 'yan sandan na Kano ya ce tuni ‘yan sanda suka cafke motar Dangoten sannan suna cigaba da bincik...