
Hukumar ICPC ta yi kira ga Matasan Najeriya Da su tashi tsaye wajan Yaki da cin hanci da rashawa
Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa, ta yi kira ga matasan Nijeriya da su zama masu karfin hali da kuma tsayawa tsaye domin yaki da cin hanci da rashawa a kowane lokaci don ciyar da kasar gaba.
Hukumar ta yi wannan kiran ne ta hannun Mai Shari'a Adamu Bello (mai ritaya), memba a kwamitin gudanarwa na hukumar.
Bello ya yi kiran ne a ranar Alhamis a Kano yayin gabatar da kyaututtuka ga wadanda suka yi nasara a gasar da hukumar ta shirya.
A yayin gasar, Faziyya Ishaq SSI daliba daga makarantar Sakandare ta Kano Capital ita ce ta lashe matsayi na 6 na gasar sannan Francis Chinedu Okolo ya zo na 3 a gasar a fagen wake-wake.