
Gwamnan Filato ya hana sallar Idi a filin Idi saidai a masallatan Juma’a
Gwamnatin jihar Filato ta hana sallar Idi a Filin Idi a jihar ta inda tace Musulmai su yi amfani da masallatan Juma'a dan yin sallar.
Gwamnan jihar, Simon Lalong ta bakin sakataren gwamnati, Farfesa Danladi Atu ne ya bayyana haka.
Yave mutane su kula da kiyaye dokokin dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19 yayin sallar sannan kuma an hana shagulgulan sallah.