
Saudiyya ta gargaɗi limamai kar su gudanar da Sallar Idi’
Ma'aikatar harkokin addinin musulunci a Saudiyya ta gargadi limamai a ƙasar da kada su gudanar da Sallar Idi, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.
Ministan harkokin addinin musulunci, Sheik Abdullatif Al-Asheikh ne ya umarci yin hakan a wata sanarwa da ma'aikatarsa ta fitar.
Wannan wani yunƙuri ne na dakatar da taruwa a masallatai kamar yadda ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar ta bada umarni domin daƙile yaduwar cutar korona.