
Da Dumi Dumi: “Hukumar yan sanda zata yiwa jami’anta karin albashi”>> Inspecta Janar na yan sanda
Hukumar yan sanda ta fara daukar matakai akan rade raden cewa wasu jami'anta na shirin tafiya yajin aikin akan rashin karin albashi.
Wanda hakan yasa Inspecta Janar Usman Alkali Baba ya bayyana cewa hukumar yan sanda zata yiwa jami'an nata karin albashi,
Kuma ya kara da cewa za'a basu sabbin kaki da kuma sauran kayan aikin da suke bukata.