fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Iikitocin Najeriya

Likitocin Najeriya sun yi barazanar sake tsunduma yajin aiki

Likitocin Najeriya sun yi barazanar sake tsunduma yajin aiki

Kiwon Lafiya
Kungiyar kwararrun Likitocin Najeriya da ake kira da NARD ta baiwa gwamnatin tarayya nan da makonni 3 ta biya mata bukatunta ko kuma ta tsunduma yajin aiki.   Sanarwar da kungiyar ta fitar ta bakin shugabanta, Aliyu Sokombo ta bayyana cewa akwai alawus na aikin Coronavirus/COVID-19 da Likitocin suka yi wanda ba'a basu ba. Sannan akwai hakkokin iyalan membobin kungiyar da suka mutu da ba'a biyasu ba duk da ikirarin gwamnati na cewa ta biya kamfanonin Inshora.   Yace wasu Gwamnatocin jihohi suma Likitocin na binsu bashin hakkokinsu dan haka sun baiwa gwamnatin nan da 17 ga watan Augusta idan bata biya musu hakkokinsu ba to zasu koma yajin aikin da suka dakatar.