
Iker Casillas: Golan Madrid da kuma Sifaniya yayi ritaya daga wasan kwallon kafa bayan ya buga wasanni kusan 1000 a rayuwar sa
Casillas mai shekaru 39, wanda ya kafa tarihin cire kwallaye masu yawa a gasar zakarun nahiyar turai da kuma kasar sifaniya ya buga sauran wasannin shi na tsawon shekaru biyar a kungiyar Porto, bayan wasannin da yayi na tsawon shekaru 25 a Real Madrid ya kare a shekara ta 2015.
Golan yayi nasarar lashe kofin duniya kuma ya lashe kofin European Championship sau biyu sannan kuma ya lashe kofin La Liga sau biyar, bugu da kari golan ya lashe gasar Champions League sau uku.
Kuma a kasar sifaniya yayi nasarar lashe Supercopa de Espana sau hudu kuma ya lashe UEFA sau biyu yayin da kuma ya lashe kofin FIFA na duniya na kungiyoyi. Kuma bayan ya koma Portugal ya cigaba da samun nasara yayin da ya lashe kofin babbar gasar su ta primeira liga. Casillas ya karbi kyautar kwararren golan La Lig...